Yadda ‘yan bindiga su ka kwashi mutum 47 yayin Sallar Tahajjud a Katsina

Karatun minti 1

Ana zargi wasu ‘yan bindiga da kutsa wa cikin wani masallaci yayin Sallar Tahujjudi, su ka sace a ƙalla mutum 47 daga cikin masallatan.

Rahotanni daga karamar hukumar Jibia da ke jihar Katsina sun tabbatar da cewa ‘yan bindugar sun afka masallacin ne wajejen karfe 2 na daren yau Litinin.

Wata majiya ta bayyana cewar ‘yan bindugar sun tusa ƙeyar mutum 47 zuwa cikin daji, sai sai wasu daga cikinsu sun samu kuɓuta.

Wani da ya buƙaci a sakaya sunanshi ya tabbatar da cewa, sun samu labarin zuwan ‘yan bindugar kuma sun sanar wa jami’an tsaro.

Ya ce jami’an sun ɗauki dukkanin matakan kariya, sai dai a cewarsa ‘yan bindugar sun canza shiri kuma hakan yana da alaƙa sun samu labarin shirin jami’an tsaro daga ɗan leƙen asirinsu.

Har yanzu dai babu wata sanarwa daga hukuma dangane da batun.

 

Karin Labarai

Sabbi daga Blog