Labarai

Majalissar Tarayya tana duba yiwuwar mayar da wa’adin mulki tsawon shekaru 6

Majalissar wakilan Najeriya ta fara duba yiwuwar yi wa kundin tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima akan wa’adin da shugaban kasa da gwamnoni suke yi a kan mulki.

Majalissar ta raja’a kan mayarda wa’adin mulki ya koma shekaru 6 a duk zangon mulki wanda babu neman tazarce.

Dan majalissar wakilai daya fito daga jihar Binuwai ne ya kawo kudirin wanda zuwa yanzu aka duba yiwuwar yi wa kudirin karatu na biyu a ranar Talata.

Kudurin ya samu taken; “Kudirin da zai canza rukunin dokar Najeriya ta shekarar 1999, wacce zata bada wa shugaban kasa, gwamnoni da ‘yan Majalissun jiha da na tarayya damar yin shekaru 6 a zango na farko wanda zai zama babu sake neman tazarce.”

Sai dai an samu rabuwar kai a tsakanin yan majalissun akan kudirin.

UA-131299779-2