Buhari Signs
Labarai

Shugaba Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin shekarar 2020

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin shekarar 2020 a yau Talata, 17 ga watan Disambar 2019.

A yau ne dai shugaban yake cika shekaru 77 a duniya, wacce tazo dai dai da ranar da shugaba ya sanya hannu a kasafin kudin Najeriya.

Naira tiriliyan 10.59 ne kudin da shugaban ya sanya wa hannu.

DABO FM ta tattaro cewa taron ya samu halarci mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, shugaban Majalissar Dattijai, Sanata Ahmad Lawan, shugaban Majalissar wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran manyan mukarraban gwamnatin Najeriya.

Shugaban ya bayyana cewa; “Yau rana ce mai dadi, na sanya hannu a kasafin kudi a ranar da nake cika shekara 77 a duniya.”

“Nayi murnar yacce Majalissar Tarayya tayi hubbasa wajen aminta da wannan kasafin cikin tsari. Yanzu tsarin kasafin kudin ya dawo Kasafin da akeyi a watan Disamba zuwa Janairu.”

Karin Labarai

Masu Alaka

Za’a kammala ayyukan filin jirgin saman Enugu, Kano, Lagos da Maiduguri a 2020 – Buhari

Dabo Online

Zaben2019: Ba abinda Buhari zai min, ko babu shi zanci zabe – Ganduje

Dabo Online

An janye karar da aka shigar don ganin kotu ta bawa Buhari damar zarcewa a karo na 3

Muhammad Isma’il Makama

Kamfe: Shugaba Buhari ya taka rawa

Dabo Online

Shin da gaske Shugaba Buhari zai kara aure?

Dabo Online

Zuwan Hanan Buhari daukar hoto Bauchi cikin jirgin saman Shugaban Kasa ya yamutsa hazo

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2