Labarai

Makarantar sakandare ta unguwa uku na barazana ga rayukan dalibai, tare da rushewar ajujuwa

Makarantar sakandare ta GGSS unguwa uku tayi kira da gwamnati Abdullahi Umar Ganduje data duba Allah ta kawo wa makarantar tallafi domin ceto rayuwar dalibai da dama domin daga yanzu zuwa ko wanne lokaci zata iya ruguzowa akan daliban makarantar.

Cikin wata tattaunawa da DOBO FM tayi da mazauna unguwar, Sanata Abba Madugu ya bayyana cewa makarantar tana cikin wani hali na innalillahi wa innailaihirrajirun, bisa yanda ginin ajujuwan ke barazanar ruguzowa a kan daliban makarantar.

Madugu ya kara da cewa “Ajujuwa da dama na bukatar gyara sannan bamu ma takamai man kujerun zama a cikin wannan makaranta, muna kuma neman tallafin gwamnati da kingiyoyin tallafawa harkar ilimi.”

Makarantar GGSS Unguwa Uku dai tana karkashin karamar hukumar Tarauni ne dake jihar Kano.

UA-131299779-2