Sheikh Dr Isah Ali Pantami – Sabon Ministan Sadarwa a Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Dr Isah Ali Pantami, a matsayin sabon Ministan Sadarwa a Najeriya.

DABO FM ta tattaro cewa; a ranar Laraba, 21 ga watan Agustar 2019, shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Shehin Malamin tare da sauran Ministoci wadanda zasu jagoranci mulki shugaban kasar a zango na biyu.

Kadan daga cikin Tarihin Dr Isa Ali Ibrahim Pantami

An haifi Dr Isa Ali Ibrahim Pantami a ranar 20 ga watan Oktobar 1972 a unguwar Pantami dake Gombe, jihar dake Arewa maso Gabashin Najeriya.

Isa Pantami ya kasance ‘da ga Mallam Ali Ibrahim Pantami, mahaifiyarshi kuwa itace Malama Amina Umar Aliyu.

DABO FM ta binciko cewa Dr Pantami ya fara karatun Al-Qur’ani a makarantar Allo kafin daga bisani ya shiga makarantar Firamare ta ‘Pantami Primary School’ inda a nan ne ya samu shaidar kammala karatun firamare, ya kammala karatun sakandire a makarantar Sakandire ta Kimiyya ta ‘Government Science Secondary School, Gombe.

Daga nan ne ya samu shigar jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) dake jihar Bauchi, inda a nan ne ya samu damar kammala karatun Digiri a fannin Fasahar Kwafuta a shekarar 2003 tare da samun Digiri na 2 duk a fannin, a shekarar 2008. Pantami ya kammala karatun Digirin-digirgir a jami’ar Robert Gordon dake Aberdeen a kasar Sukotlan.

Masu Alaƙa  Sheikh Pantami yayi kira da acigaba da goyawa Buhari baya don cigaban Najeriya

Ya fara aiki a jami’ar ATBU, inda yake koyar da ‘Information Technology’ kafin daga bisani ya koma Jami’ar Musulunci dake Madinah a matsayin shugaban Rubutun Fasaha a shekarar 2014.

A shekarar 2016, Pantami ya ajiye koyarwa, inda a nan ne shugaba Muhammad Buhari ya nada shi ya zama shugaban hukumar ‘NITDA’ a ranar 26 ga watan Satumbar 2016.

Ya kasance babban malamin addinin Musulunci na sama da shekaru 20, ya kasance limamin sallah Juma’a a Najeriya da kasar Birtaniya.

Sako na musamman

Shin kuna da wata sanarwa ko bukatar bamu labari?

Ku aiko mana da sako ta submit@dabofm.com

%d bloggers like this: