Labarai Nishadi

Maryam Booth za ta raba buhuhunan Shinkafa, Mai da sauran kayayyakin abinci

Fitacciyar jarumar fim ta Kannywood, Maryam Booth zata raba kayyakin abinci ga masu tsananin bukatar taimako dake sansanin yan gudun hijira.

DABO FM ta tattara cewar kayyakin abincin sun hada da buhuhunan Shinkafa, galan din Mai da kuma Farin Magi.

Jarumar ta bayyana haka ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter a yau Lahadi, 29 ga watan Maris din 2020.

“Zan bayar da kyautar buhun Shinkafa guda 100, galan na Mai guda 50 tare da katan 100 na ‘Farin Magi’.”

“Idan kun san sansanonin, ku rubutamin adireshin, zamu je.”

Haka zalika Maryam Booth tace zata bayar da kyautar kayyakin abincin ne ga mutanen da suke a sansanonin ‘yan gudun hijira masu tsananin bukata, har ma nemi mutane da su bata adireshin sansanonin da suka sani wadanda aka san suna da bukatar kayan.

A kwanakin baya DABO FM ta tattara cewar mawaki Ali Jita, ya rabawa Almajirai rigunan sanyi hadi da wasu kayayyakin abinci.

A yayin zantawarmu dashi ya bayyana mana cewar ya raba kayayyakin ne a unguwar Zoo Road dake Kano.

Karin Labarai

Masu Alaka

Kannywood: Mawakan APC sun zargi Rarara da handame kudaden kungiyar da aka tara

Dabo Online

Ali Jita ya raba wa ‘Almajirai’ rigunan sanyi da barguna

Dabo Online

Zamani Riga: Me duniyar Kannywood take ciki a Yau da nasarorinta?

Dabo Online

Kotu ta bayar da belin Sunusi Oscar 442

Dabo Online

Darakta Hassan Giggs zai dauki nauyin yi wa wani matashi tiyatar ido

Dabo Online

‘Yan Bindiga sun sace ‘dan uwan Sani Mu’azu, gwamnan ‘Alfawa’ na shirin ‘Kwana Casa’in’

Dabo Online
UA-131299779-2