0
Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 14 da daren yau Lahadi.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 111.
“A daren yau da misalin karfe 9:30, an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda14.”
Hukumar tace an sake samun 9 a jihar Legas, 5 a Abuja wanda ya hada jimillar wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 111.”
Jerin adadin da aka tabbatar a kowacce jiha;
- Lagos- 68
- Abuja- 21
- Ogun- 3
- Inugu- 2
- Ekiti- 1
- Oyo- 7
- Edo- 2
- Bauchi- 2
- Osun-2
- Rivers-1
- Binuwai- 1
- Kaduna- 1
