A yau Litinin wata Kotu a Abuja ta kawo karshen shari’ar da aka dauki tsawon lokaci sama da shekara ana gudanarwa.
DABO FM ta tattara cewar kotun ta tabbatar da zargin da ake yiwa Maryam Sanda na kashe mijinta, Bilyaminu Usman.
A daidai lokacin da alkali yake tabbatar da laifin kisan da ta aikata, Maryam Sanda ta tsere daga zauren kotu.
Sai dai Daily Trust ta tabbatar da cewa jami’an tsaro da jami’an kula da gidajen yari suka tiso keyarta ta dawo zauren Kotu.
Biyo bayan kururuwa daga wasu mata a cikin kotun, alkali ya tafi hutu mintuna biyar wanda da zarar ya dawo, zai yanke mata hukunci.
An dai jiyo Maryam Sanda tana cewa “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un’ har ma tana cewa “Ina ta azumi da Sallah……. Ya Allah”
