Home LabaraiYanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa

Yanzu-Yanzu: Kotu ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa

by Dabo Online
0 comments

Wata babbar Kotu dake Abuja ta yanke wa Maryam Sanda hukuncin kisa bayan tabbatar da zargin da ake mata na kashe mijinta, Bilyaminu.

A ranar 19 ga watan Nuwambar 2017 ne dai Maryam Sanda ta kashe mijinta ta hanyar luma masa wuka a ciki, kamar yadda Kotu, Yan sanda da shaidu suka tabbatar.

Mai shari’a, Yusuf Halilu ya bayyana cewar dukkanin hujjoji sun tabbatar da Maryam Sanda ta aikata laifin da ake tuhumarta dashi na kashe mijinta a shekaru 2 da suka gabata.

Bayan tabbatar da laifin kafin yanke hukunci, kururuwar wasu Mata ta tilastawa alkalin tafiya hukutun mintuna 5 kafin ya yanke hukuncin.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00