Masarautar Rano ta hukunta Hakimai da sukayi wa sarkin Kano Sunusi mubaya’a

Masarautar Rano dake jihar Kano ta hukunta wasu hakimanta da suka bijerewa umarnin Sarki.

Hakiman garin Bebeji dana Tudun Wada ne suka karbi hukunci dakatarwa daga masarautar.

A cikin wata takada mai lamba REC/HD//1/VOL1/006 da REC/HD//1/VOL1/004 dauke da sa hannun sakataren masarautar Rano, Muhammad Idris Rano, tace ta dakatar da hakiman Bebeji da Tudun Wada kamar yadda Dabo FM ta tattaro.

Masarautar Rano tace sun bijirewa kira da Sarkin Rano, Alhaji Tafida Ila, yayi musu na zuwa gaisuwar Sallah tare da kawo dawaki da jama’arsu domin yin hawa salla a yankin na Rano.

Sai dai hakiman sun bijirewa umarnin inda suka kai gaisuwarsu ga Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, tare da yin hawan sallar Idi da hawan Daushe da aka gudanar a jihar.

ZUwa ga Hakimin Tudun Wada
%d bloggers like this: