Buhari ya kira Ganduje zuwa Abuja akan rikicinshi da Sarki Sunusi

A karshe dai shugaba Muhammadu Buhari ya shiga tsakanin rikicin dake tsakanin Gwamna Ganduje da Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II.

Hakan na zuwa ne a lokacin daya rage saura wa’adi da gwamnatin Kano ta bawa Sarki Sunusi daya kare kanshi akan batun ta’annatin kudin masarautar.

DaboFM ta binciko cewa tin dai a farko farkon dara dambarawar ne, al’umma sukayi ta kira akan shugaba Buhari da sauran manyan Arewa su shiga tsakani.

Majiyoyi masu tushe daga fadar gwamnatin tarayya sun bayyanawa Jaridar Daily Nigerian cewa shugaba Buhari baya farinciki da abinda yake faruwa a jihar Kano.

“Shugaba Buhari bai cika shiga al’amuran jihohi ba. Amma akan wannan matsalar, shugaban kasa zai shiga tsakani.”

“Shugaban Kasa baya jin dadin abinda gwamnan yayi na yanke hukuncin rarraba masarautu tare da yunkurin cire sarkin.

“Shugaban kasa ya kira Ganduje a ranar Alhamis tare da umartar darakta jami’an DSD daya kira taron gwamnonin yankin Yammcin Arewa na gaggawa.”

Gwamnonin da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El-Rufai, yake jagoranta, ya fara kaiwa shugaban kasa bayanai kan abinda yake faruwa a ranar Alhamis.”

Shugaban kasa ya kira Sarkin na Kano, Muhammadu Sunusi II, tare da Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani a ranar Juma’a.

%d bloggers like this: