Ganduje na daf da dakatar da Sarki Sunusi da yiwuwar maye gurbin masarautar Kano da Aminu Ado Bayero

Biyo bayan aike da takardar tuhuma da gwamnati Dr Ganduje ta aikewa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II akan kashe kudaden masarautar Kano ta gwamnatin ta kira ta’annati.

Majiyoyi sun tabbatar da aike takardar zuwa ga Sarkin Kano, tare da bawa sarkin Wa’adin sa’o’i 24 ya kare kanshi daga tuhumar da ake masa.

Majiyoyi sun tabbatar da shirin gwamnatin jihar Kano akan dakatar da Sarki Muhammadu II, tare da dawo da Sarkin Bichi, Alhaji Aminu Ado Bayero domin jagorantar masarautar Kano.

Dabo FM ta gudanar da bincike daya tabbatar da gwamnatin Ganduje tafi bada muhimmanci ga masarautar Bichi wacce Alhaji Aminu Ado Bayero yake yiwa Sarki, bisa fitar da makudan kudaden wajen gina sabuwar masarautar, siyan manyan motoci na alfarma da zasu lashe miliyoyin Nairori duk da rashin ingantaccen Ilimi da Ruwan sha a jihar Kano.

Ganduje zai iya nada Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama Sarkin Kano bisa dalilan da gidan Dabo FM ya zakulo;

* Sabuwar dokar masarautun da majalissar Kano tayiwa gyara, tace Sarkin kowacce masarauta zai iya mulkar masarautar Kano ta zarar ya zama shugaban

*Dokar tace kowanne Sarki yana da damar zama Sarkin Kano idan bukatuwar hakan ta taso.

*Dokar tace za’a iya chanzawa Sarakunan masarautu duk bayan shekaru 2.

Da wadannan dalilan dokar, muka tattara tare da fitar da bincikenmu a nan Dabo FM, musamman yadda mukaji daga bakin wasu jagororin gwamnatin Kano inda bayyana cewa gwamnatin tana shirin maye gurbin Aminu Ado Bayero da Sarkin Muhammadu Sunusi II.

Tini dai Ganduje ya aike da takardar tuhuma zuwa ga Sarki Sunusi bisa bata da kashe kudaden masarautar ba bisa ka’ida ba, inda kuma gwamnan ya bashi awanni 48 domin ya kare kanshi dage tuhumar.

Lamarin dai yayi tsamari tsakanin masarautar ta Kano da tsagin gwamnatin Ganduje, hakan ne yasa gwamnatin ta kirkiro sabbin masarautu 4 domin rage darajar Sarki Sunusi daga iko da kananan hukumomi 44 zuwa guda 10 kacal.

%d bloggers like this: