Aminu-Bello-Masari-
Labarai

Masari ya amince a cigaba da gabatar da Sallar Juma’a a jihar Katsina

Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya aminceda gabatar da Sallar Juma’a da zuwa Coci a ranakunJuma’a da Lahadi a fadin jihar.

Sakataren gwamnatin jihar ta Katsina, Alhaji Mustapha Inuwa ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Najeriya ‘NAN’ ya rawaito.

Sanarwa tace gwamnaan ya dage dokar haramta yin doguwar tafiya tsakanin kananan hukumomin jihar.

Gwamnan ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su cigaba da bin dokokin domin kariya daga kamu daga cutar Kwabid-19.

DABO FM ta tattara cewar matsalar tsaro a jihar Katsina tayi tsamarin gaske inda al’ummar jihar suke ta bayyana kukansu game da matsalar tsaron jihar.

Karin Labarai

UA-131299779-2