Babban Labari Labarai

Mun tallafawa al’ummar ne ganin halin da ake ciki-Hassan Rilwanu

Al’ummomi sama da 1000 ne da suka fito daga kananan hukumomin Zariya da Sabon Gari a Jihar Kaduna, suka amfana da kayan hatsi da kuma naman sallah kyauta daga shugaban hukumar bada tallafin karatu ta Jihar Kaduna Alhaji Hassan Rilwanu.

Rabon kayan tallafin wanda ya gudana tun a bikin sallah karama da ta gabata, an raba shinkafa da naman sallah ga mutum 100 da suka amfana a gundumar Gyallesu kadai, yayin da mutane da dama suka amfana a yankin karamar hukumar Sabon Gari.

Da yake karin hake game da rabon tallafin, shugaban hukumar bada tallafin karatun ta Jihar Kaduna Malam Hassan Rilwanu, ya ce, makasudin fito da wannnan tsari na bada tallafi, shi ne ganin yadda mutane ke cikin wani yananyi, musamman saboda zaman gida da suke bayan da gwamantin Jihar Kaduna ta sanya dokar takaita zirga-zirga saboda cutar sarkewar numfashi ta Covid-19 da ta addabi sassan duniya, kuma a matsayin su na wanda suke da mukami a cikin gwamnati, dole ne su naimi hanyoyin tallafawa mabuka saboda rage ma gwamnati wani nauyi da ya rataya a kanta.
Kasancewar gwamnati ba ta iyawa ita kadai, dole ne sai ire-iren sa da sauran al’umma sun dukufa wurin lalubo hanyoyin taimakon gwamnati.

Kana ya tabbatar da manufar sa na fadada shirin badatallafin zuwa wasu kananan hukumomi da ke Jihar Kaduna.

A cewar Hassan Rilwanu, tunda Allah ya sa yana cikin gwamnati, ya san irin kokarin da gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmed El-rufa’i ta ke yi domin wadata al’umma da ababen more rayuwa, da kuma irin manufofin da yake da su domin dakile yaduwar cutar Covid-19 a fadin Jihar sa.

Ya kara da cewa, sun bi hanyoyi da dama wurin zakulo hazikan jagorori da za su shige gaba, domin ganin tallafin ya kai ga wanda aka tanada domin su, kamar kansila mai wakiltar mazabar Gyallesu Hon Aminu Sani Minista da ire-iren sa.

Kuma zuwa yanzu sun gamsu da yadda al’umma suka karbi tallafin.

Da yake jawabi a madadin al’ummar mazabar sa, kansila mai wakiltar mazabar Gyallesu a majalisar kansilolin karamar hukumar Zariya Hon Aminu Sani Minista, ya fara ne da jajantawa al’umma bisa halin da ake ciki na kulle, kuma ya ce hakan ana sa ran zai saukaka yaduwar cutar kamar yadda gwamnati ta dauki matakan da suka dace.
Kuma ya gode ma Malam Hassan Rilwanu saboda zaban gundumar sa ya kawo irin wannan tallafin, ya ce, an tsara mutane da dama ne za su amfana da tallafin, amma ganin halin da al’umma ke ciki sai aka shirya baiwa wasu kayyadaddun mutane saboda abun da za su samu ya zama mai tsoka.

Wasu daga cikin wanda suka amfana da tallafin, Malama Amina Lawal da Malam Atiku Abdullahi, sun nuna matukar farin ciki ne tare da godiya ga shugaban hukumar bada tallafin karatun ta Jihar Kaduna Malam Hassan Rilwanu, kuma suka yi addu’a Allah ya saka da mafificin Alheri.

Karin Labarai

UA-131299779-2