//
Sunday, April 5

Shekaru biyar da rashin Dan Ibro: Waye ya maye gurbinshi?

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Rabilu Musa , wanda aka fi sani da Dan Ibro, fitaccen jarumi, jarumin barkwanci, mashiryin fim hakazalika mai bayar da umarni, ya kasance dan wasan barkwanci da masa’antar Kannywood bata taba samu ba har zuwa mutuwarshi a shekarar 2014. Tin daga lokacin, mutane suka shiga tunanin ko waye zai iya takar rawar da marigayi dan Ibro ya taka.

Ranar 9 ga watan Disambar 2014 itace ranar da masana’antar Kannywood bazata taba mantawa da ita ba. Itace ranar da jarumi Dan Ibro ya koma ga Allah.

Tin daga lokacin, an bar wa Kannywood aiki mai tarin wahala na nemo wanda zai cike gurbin Dan ibro daga cikin jaruman da suke taka rawa a cikin masana’antar yanzu.

Masu Alaƙa  Gobara a Kannywood: Mun sasanta da Mustapha Nabruska - Hadiza Gabon

Ana ganin cewar baza’a taba iya samun wanda zai cike gurbin jarumin ba. A wani bangare kuma, wasu na gani lokaci zai zo da za’a samu wanda zai maye gurbin marigayi Ibro.

Dan Ibro da ake kiranshi da ‘Chairman’ ya kasance gwarzon da yake iya mayar da kowanne motsi ya zama na barkwanci. A lokacinshi, ya zama babban Wa a wajen jaruman kungiyar.

Ya shirya fina-finai masu tarin yawa a karkashin kamfaninshi, Ibro Drama Group wanda fim din ‘Andamali’ ya zama fim na karshe da kamfanin yayi kafin rasuwar Dan Ibro. Bayan rasuwarshi, kamfanin ya dena aiki.

Karin Labarai

Share.

About Author

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020