Home LabaraiMasu kwacen waya a Kano sun caccaka wa wani almakashi da adda a kirji

Masu kwacen waya a Kano sun caccaka wa wani almakashi da adda a kirji

by Dabo Online
0 comments

RAJASTHAN: Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano sun bayyana kama wasu mutane biyu da aka zarga da caccaka wa wani mutum almakashi da adda a kirji, suka kuma kwace masa waya.

Mai magana da yawun rundunar reshen jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.

Ya ce wadanda ake zargi sun haura gidan wanda suka caccakawa almakashin ranar 7 ga watan Yuni da misali karfe 3:00 na asuba a unguwar Wailari dake cikin birnin Kano.

Sai dai har zuwa yanzu rundunar bata bayyana sunayen wadanda suka yi aika-aikar ba.

Ya tabbatar da cewar sun caccakawa mutumin mai suna Ibrahim Adamu almakashi da zabgegiyar adda a kirji su ka tafi da wayarshi wanda hakan ta sanya ya samu munanan ciwuka a jiki.

“Bayan samu labarin al’amarin, mun aike da jami’anmu zuwa wajen tare da daukan mutumin zuwa babban asibiti na Murtala Muhammad inda yake karbar magani.

“Mun kama wadanda ake zargi da adda da almakashi a tare da su.”

DSP Haruna Kiyawa ya bayyana cewar tini dai kwamishinan ‘yan sandan Kano, CP Habu Ahmad, ya bayar da umarnin aike su sashin binciken kwakwaf domin yin bincike.

Ya tabbatar da cewa da zarar an kammala bincike, za a aike da su zuwa kotu domin fuskantar hukunci.

You may also like

-
00:00
00:00
Update Required Flash plugin
-
00:00
00:00