RAJASTHAN: Shugaba Muhammad Buhari ya jinkirtar da dokar bai wa ‘yan majalissun jihohi da bangaren shari’a damar cin gashin kansu, cewar Mista Kayode Fayemi, gwamnan jihar Ekiti.
Gwamnan ya bayyana haka ne ya yi zantawa da manema labarai jim kadan bayan fitowarsu daga tattaunawa da wasu gwamnoni, ministoci da shugaban ma’aikatan fadar shugaban Buhari, Ibrahim Gambari a ranar Litinin, kamar yadda Premium Times ta rawaito.
DABO FM ta tattara cewar a ranar 22 ga watan Mayu, shugaba Buhari ya sanya hannu a dokar da zata bai wa ‘yan majalissun jihohi da banagren shari’a damar cin gashin kansu ta bangaren kudi.
Dokar dai za ta haramtawa gwamnonin jihohin Najeriya samun damar taba wa ko rike kudin ‘yan majalissar jiha, hakazalika za ta haramtawa gwamnonin taba kudin bangaren shari’a a kowacce jiha.
Gwamna Fayemi ya ce shugaba Buhari ya dakatar da aiwatar da dokar bayan ya sanya wa dokar hannu a watan Mayu.
“Mu aika wakilai daga kungiyar gwamnoni domin tattaunawa da shuagan kasa akan wannan batun. Ya ce mu je mu gana da Minstar Kudi da kasafi, Babban mai shari’a na kasa da kuma shugaban ma’aikatan shugaba Buhari.”
“Mun zauna akan batun da kuka dade kuna tattaunawa akai ku manema labarai, akan maganar bai wa ‘yan majalissun jiha da bangaren shari’a cin gashin kansu, mun sami ganawa da shugaban kasa kafin yanzu kuma ya nuna jin dadinshi bisa hadewar kan gwamnoni waje guda domin duk muna goyon bayan cin gashin bangarorin guda biyu.”
“Sai dai matsalar tana yadda za a aiwatar da dokar wanda bai dace da kundin tsarin mulkin kasa ba, duba da haka shugaban kasa ya ce za a jinkirtar da zartar da dokar kuma ya bada umarnin ganawa da babban mai shari’a na kasa da Ministar Kudi.”, inji Fayemi, shugaban kungiyar gwamnoni.
Fayemi ya kara da cewa tini gwamnonin suka shiga cikin tattaunawa da shuwagabannin majalissar jihohinsu domin ganin lallai sun samu gashin kan nasu.
“Muna ta tattaunawa da wakilan shuwagabannin majalissa na kowacce jiha. An nada mataimakin kungiyar gwamnoni, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal domin jagorantar namu wakilan da suka taba rike wata kujera a zauren majalissa ko suka taba yin Sanata ko majalissa tarayya domin tattaunawa da wakilan shuwagabannin majalissar jihohin, kuma mun yi imani cewa zamu shawo kan matsalar ba tare da ta kai ga zuwa kotu ba.
WAsu daga cikin mahalarta zaman sun hada da Ministar Kudi, Hajiya Zainab Ahmad, babban mai shari’a na kasa, Abubakar Malami, Aminu Waziri Tambuwal da takwaranshi, Abubakar Bagudu, gwamnan jihar Kebbi.
DABO FM ta tattara cewar Cikin wata takarda da babban mai shari’a na Najeriya ya fitar, ta ce dole ne gwamnonin jihohi su rika sanya kudaden bangarorin biyu a cikin kasafin kudin jiha, a matsayin abinda yake dole gareta.
Hakazalika dokar ta ce za a ware wa bangaren shari’a kudaden da zasu rika kula da gyaran kotuna da guraren da suke aiki.
Jinkirta dokar na zuwa ne bayan da gwamnoni suke nuna kin amincewarsu ga dokar.
