Kotun Koli ta karbe kujerar gwamna daga PDP ta bawa APC mai mulki

Kotun kolin Najeriya, ta tsige gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha daga matsayinshi na gwamnan jihar Imo, ta tabbatar da Sanata Hope Uzodimma na APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.

Shari’ar da alkalai 7 suka jagoranta sunce ba’a zabi gwamna Emeka Ihedioha ba.

Kotun ta umarci hukumar INEC ta karbe takardar shaidar lashe zabe da aka bawa gwamna Ihedioha, ya kuma gaggauta sauka daga kan mulkin jihar.

Haka zalika ta umarci hukumar ta bawa Sanata Hope Uzodimma shaidar lashe zaben tare da gaggauta rantsar dashi.

Masu Alaƙa  Kano: Kotun daukaka kara ta tabbatar wa Hon Shamsuddeen Dambazau na APC kujerarsa

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.