Labarai Ra'ayoyi

Matakin Atiku na daukaka kara yayi dai-dai da tsarin Dimokradiyya – Barista Jafaru Abbas

Mu’azu Albarkawa , Kaduna.

Jafaru Abbas, lauya kuma masanin kudin tsarin mulkin kasa, ya bayyana matakin da Alhaji Atiki Abubakar, ya dauka na zuwa kotun koli a matsayin “Yin abinda ya dace.”

Lauyan ya bayyana hakane yayin ganawarshi da wakilin DABO FM a garin Zaria na jihar Kaduna.

“Matakin da Jam’iyyar PDP da Dan takarar ta na shugaban kasa Alh Atiku Abubakar, suka dauka na daukaka kara zuwa kotun gaba, mataki ne da ya dace.”

“Yin hakan zai cigaba da bunkasa Dimokradiyyar kasar nan.”

Ya ce, daman kotu na da damar watsi da karar da aka shigar gabanta, sai dai abun da ake la’akari da shi, shi ne ingancin dalili da wannan kotu ta dogara a kai.

Ya kara da cewa, hukumcin kotun ba shi ke nuna kawo karshen shari’a ba, illa ra’ayi ne na Alkalan da suka jagoranci shari’ar.

A cewar shi, irin yadda aka yi amfani da Jami’an tsaro da hukumar shirya zabe mai zaman kanta ta kasa, mataki ne da a fili ke nuna karara yanda aka murde zaben shugaban kasan da ya gabata.

“Abinda ‘yan Najeriya suka gani a lokacin zaben da ya gabata ya nuna a zahirance ba wani hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, kuma hukumar zaben wata bangare ce ta gwamnatin APC” inji Jafaru Abbas.

A karshe ya bayyana cewa yana fatan daukaka karar da Alhaji Atiku Abubakar da jami’iyyarshi ta PDP sukayi, zata canza zani tare da samun hukuncinda zai gamsar da ‘yan Najeriya.

A larabar da ta gabata ne dai kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa ta tabbatar da zaben da aka yi wa dan takarar Jam’iyyar APC Muhammadu Buhari, kuma ta yi watsi da karar da Jam’iyyar PDP da dan takararta Atiku Abubakar suka shigar suna kalubalantar zaben.

Hukumcin da Jam’iyyar APC ta ce ya yi mata dai-dai kuma ta san za’a rina.

Karin Labarai

UA-131299779-2