Labarai

Pantami ya bada umarnin rufe layuka miliyan 9 da ake siyarwa ‘Masu Rijista’

Ministan Sadarwa na Najeriya, Dr Isah Ali Pantami ya baiwa hukumar kula da harkokin sadarwar ta NCC umarnin kulle layukan da ake siyarwa masu Rijista.

Ya bayyana a rufe layukan har sai wadanda sukayi rijista sunzo da shaidar cewa layukan nasu ne.

Dr Pantami ya bayar umarnin ne yayin da yake da yake karbar bakuncin bangaren zartawa na Majalissar kwararrun masu amfani da kwamfuta CPN da NCS, a wata ziyarar da suka kai masa a ofishinshi dake Abuja, kamar yacce Daily Nigerian ta tabbatar.

Ziyarar da suka kai wa Ministan ta taya murna bisa bashi mukamin Ministan ma’aikatar sadarwa tare da nuna goyon bayansu ga shirin Ministan na ciyar da bangaren Na’ura mai kwakwalwa a Najeriya.