Labarai

Matashi ya alkauranta raba Naira Miliyan 4 idan Atiku yayi nasara a Kotu

DABO FM ta binciko wani matashi yayi alkawarin rabawa mutane 20 Naira miliya 4 idan Alhaji Atiku Abubakar yayi nasara a kotun zabe.

Matashin, Aliyu Dahiru Bello, dan asalin jihar Gombe, ya bayyana haka ne a shafinshi na Twitter a ranar Laraba da kotun sauraren korafin zaben shugaban kasa zata yanke hukunci zaben da Atiku Abubakar yake kalubalanta.

Rubutun matashi ya ja hankalin mutane musamman masu amfani da manhajar Twitter inda mutane 1,774 suka magantu akan rubutun. (Adadi a lokacin da muke hada rahotan).

Sai dai tin tuni alamu suka nuna Atiku zai yi rashin nasara a kotu biyo bayan watsi da ikirarin Atiku na an tafka magudin zabe a zaben daya gabata.

Abinda ake ganin shine makasudin zuwan Alhaji Atiku Abubakar kotu.

UA-131299779-2