Copyrighted.com Registered & Protected

Miliyoyin mata sun roki Atiku ya kwance damarar zuwa Kotu

Wasu mata da adadinsu ya kai miliyan biyu sun fito zanga zangar lumana domin rokon tsohon dan takarar shugabancin kasa karkashin jami’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar daya janye kalamanshi da zuwa kotun koli.

Matan sun bukaci Atiku daya kira shugaba Muhammadu Buhari domin yi masa murnar cin nasarar zabe.

“Yakamata ya dauki kaddara ya kuma karbi rashin nasara domin an gudanar da zabe sahihi.”

An gudanar da zanga zangar lumanar a yau Juma’a, 1 ga watan Maris 2019 a babban birnin tarayyar Abuja.

%d bloggers like this: