0
Zababben shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari yace zangon mulkinshi na biyu zai fi tsanani.
Shugaba Buhari yayi wannan furuci jiya, a wata ganawa da yayi da mukarraban gwamnatinshi a fadar Vill dake babban birnin tarayyar Abuja.
“Kar mutane su manta abinda na fada musu a wajen yakin neman zabe, akan habaka tattalin arziki, samar da aikin yi, tsaro da kuma cin hanci da rashawa, shekarar hudun da zamu shiga zatafi tsanani tare da tsaurarawa.”
A ranar Larabar data gabata ne dai hukumar zabe ta INEC ta bada tabbacin lashe zaben shugaba Muhammadu Buhari bayan da ya samu gagarumar nasara akan jami’iyyar hamayya ta PDP.
