Sun. Oct 20th, 2019

Dabo FM Online

World’s First pure Hausa online Radio

Yunƙurin ceto ilimin jihar Kano, daga Umar Aliyu Fagge

3 min read

Sanin kowa ne cewa ilimi shi ne jigon rayuwar alumma a kowane matakin rayuwa, babu wata alkarya da zata samu cigaba ko kuma ta zama abin kwatance a idon duniya ba tare da samun ingantaccen yanayin koyo da koyarwa ba. harkar ilimi abu ne da ya kamata a bashi kulawa matuka gaya.

Jihar kano ta kasance jiha mai dumbin tarihi a arewa maso gabashin kasar nan dama duniya baki daya, a shekarun baya da suka gabata jihar kano ta zama madubin sauran jihohi a Najeriya ta fuskoki daban-daban misali:-

#ILIMI:- harkar ilimi abu ne mai matukar muhimmaci ga rayuwar alumma gurin samar da cigaba mai daurewa, duk alummar da ta rayu cikin ilimi zaka sameta cikin kwanciyar hankali da nutsuwa. Mawuyacin abu ne ka samu mutane masu ilimi na aikata mummunar ta’adar daba, shaye-shaye ko banbadanci a cikin alumma.

Gwamnatin baya tayi kokari gurin ganin cewa alummar jihar kano ba a barta a baya ba gurin nemawa dalubai gurbin karatu a gida da wajen kasar nan, don ganin cewa mun samu nagartattun manyan gobe.

Abin takaici da koma baya sai gashi Gwamnatin da ta gaji Gwamnatin baya, tayi watsi da dukkan kokarin da akayi na ganin cewa matasan mu, an killace su daga shiga mummunar ta’adar shaye-shaye ta hanyar basu tallafin karatu da nema musu guraben karatu a makarantu. Yanzu a maimakon kaga ana tsere da dalibi gurin zuwa makaranta, sai dai kaga ana tsere dasu gurin shaye-shaye da bangar siyasa!

Wani babban wulakanci ma shi ne, da wannan Gwamnatin ta tashi bada tallafin karatu sai ta nuna bata san cewa dan talaka yana bukatar kulawar ta ba. Sai ta dauki tallafin miliyan ashirin ta bawa wata diyar gwal dake makarantar {Twins Gwarzo} kawai don yarinyar taci kiredit tara {9 credits}! Wannan kama-karyar da me tayi kama?

A daidai lokacin da ya kamata ace dalibai suna cikin ajujuwan su, sai gashi wasu daga cikin malamai sun buge da koyawa yayan talaka, kuma yan firamare zanga-zanga {protests} akan za’a tuhumi badakalar dalar amurika miliyan biyar 💰💵💵💵🤦

Tabbas a rayuwa an ha’inci tare da yaudarar iyayen daliban nan da kuma ita kanta hukumar makarantun firamare, idan har ba da sanin su akayi hakan ba. Ina mai amfani da wannan damar gurin kira ga daukacin iyaye da suyi amfani da kuri’un su gurin nemawa yayansu makoma ingantacciya, tunda dai shi da na kowa ne kuma babu iyayen da zasu so ace ga yayansu suna tanbele a titi.

Allah ya bamu Gwamna nagari wanda zai hidimta mana baki daya👏👏👏

Bawan alumma.
Umar Aliyu fagge.

©2019 Dabo FM Online. Sponsored by Dabo Media Group | Newsphere by AF themes.