Gwara dan Ak*yar da zai ga mutane ya kauce hanya ya basu wuri – Sheikh Abdullah Gadon Kaya

A wani sabon faifen bidiyo da Sheikh Abdullah Gadon Kaya ya fitar da matsayin raddi ko martani ga abinda ake zargin Yan Kwankwasiyya da yiwa Ministan Najeriya ihun, yayi kakkausar suka.

Sheikh Abdallah yayi suka tare da yin raddi kai tsaye zuwa ga shugaban matasan da aka zarga, Rabi’u Kwankwaso.

“Duk wanda yake nema a wajen wani ba Allah, kuma yana ganin zage-zagenshi da suruntanshi ne zai bashi dama, wallahi baya gamawa lafiya sai dai a kaskance a tozarce.”

“Duk wanda yabi hanya ta mutunci, zai kare da mutunci. Duk wanda yabi hanya ta rashin mutunci, daman bashi da mutunci kuma a rashin mutunci zai kare.”

Masu Alaƙa  Yazamana dole 'yan siyasa sun girmama Sarakunan Gargajiya - Dr Pantami

“Mai kima da daraja a cikin mutune, shine yasan darajar mutane, musamman wanda yake neman mutane. Amma marar mutunci dan Akuya, shine bai san mutunci mutane ba.”

“Wallahi wani lokacin gwara dan Akuya, in yazo ya tarar da mutane ma, ya kauce ya basu guri.”

Daga nan Malamin yayi addu’ar rokon Allah da cewa “Duk wanda yaci mutuncinmu, Allah ka karya shi.”

Karin Labarai

Leave a Reply

Your email address will not be published.