/

Mun dauki matakan da suka dace domin dawowar dalibai-Injiniya Kabir Abdullahi

dakikun karantawa

A shirye-shiryen ta na cigaba da gudanar da harkokin karatu tun bayan rufe makarantu kusan watanni bakwai da suka gabata saboda barkewar annobar Covid-19, makarantar kimiyya da fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya ta samar da wasu tsare-tsare domin inganta walwala da jin dadin dalibai da malamai da ma sauran ma’aikatan makarantar.

Shugaban makarantar Injiniya Dr Muhammad Kabir Abdullahi ya bayyana hakan sa’ilin da yake bayyawa manema labarai shirye-shiryen su na bude makarantar da kuma cigaba da aka samu a fannoni daban-daban.

Ya ce, an tsara dawowan ne a matakai biyu, na farko shi ne na dalibai yan ajin karshe wanda aka tsara za su dawo tun a ranar Litini 2 ga watan Nuwamba su gudanar da karatu na tsawon mako Uku kafin daga bisani kuma su rubuta jarabawa a watan Disamba mai zuwa.
Sai mataki na biyu da aka tsara dawowar su a Bakwai ga watan Disamba su ma su yi karatu tare da rubuta jarabawa a da zaran an dawo hutun sabuwar shekara.

A cewar shugaban makarantar, an samar da tsare-tsare domin cika matakan da gwamanti ta shimfida na kariya daga cutar Covid-19, inda aka umarci duka azuzuwan da adadin su ya haura Dari su raba ajin gida Biyu.
Kuma bisa agajin wasu kudade da suka samu daga gwamnatin Jihar Kaduna sun samar da kayayyakin wanke hannu a sassan makarantar, tare da raba kyallen rufe fuska ga daliban da suka fara dawowa saboda cika matakan da gwamantin Jiha ta basu na samar da wadannan abubuwa kyauta.

Injiniya Kabir Abdullahi,ya kuma yi karin haske game da cigaban da makarantar ta samu zuwa yanzu musamman game da ayyukan shimfida tituna da gine-gine da suka samu daga gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin gwamnan Nasiru El-rufai, Kuma ya ce hakan ya taimaka wurin kara bunkasa harkar koyo da koyarwa a makarantar.

A kwanakin baya sashin koyar da kere-kere ta kwalejin ta samar da wata naburar zamani ta gwada zafin jiki da kuma ta wanke hannu domin yakar annobar Korona, Kuma tuni suka aike da tsarin naburar ga ma’aikatar Ilimi ta jiha.

Injiniya Kabir Abdullahi, ya bukaci dalibai da sauran ma’aikatan makarantar su cigaba da bin matakai da ka’idojin da aka shimfida domin kariya daga cutar Korona.
Kuma ya yaba ma gwamantin Jihar Kaduna da ma’aikatar harkokin Ilimi saboda irin gudunmuwar da suke bayarwa domin cigaban makarantar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog