Maganar Gaskiya: Ba zamu iya biyan albashin ma’aikatu 428 a watan Nuwanba ba – FG

Karatun minti 1

Gwamnatin Tarayya ta bayyana ma’aikatun ta 428 baza su iya biyan albashi a ƙarshen watan da muke ciki na Nuwamba ba sakamakon kuɗin da aka ware musu na albashi sun ƙare tas.

Darakta Janar na ofishin kasfin kuɗi, Ben Akabueze shine ya bayyana wa Dabo FM bayan bayyanar sa a gaban kwamitin Majalisar Dattijai dake kula da asusun gwamnati.

Ben Akabueze ya bayyana mana cewa “Wannan yazo ne sanadiyar rashin saka tsarin mafi karancin albashi a kasafin kudin shekarar da ta gabata, 2019.”

Ya kuma kara da cewa “Gwamnati zata cike wannan gibi daga asusun ta wanda zai bada damar biyan albashin waɗannan ma’aikatun.”

Sai dai kuma shugaban kwamitinkwamitin, Senator Mathew Urhoghide ya dora wannan alhaki wannan akan kwamitin zartarwa.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog