Rundunar sojin Najeriya ta jaddada kudirin ta na cigaba da sanya horo da kwarewa ga Jami’anta

dakikun karantawa

A kokarin ta na cigaba da sanya kaimi da horo gami da kwarewa a jikin dakarun sojin Najeriya, rundunar sojin ta horas da jami’an ta 150 da suka sami kwarewa a fannoni daban-daban domin cigaban da fuskantar kalubalen da ke gaban su wurin tafiyar da wanzuwar kasar nan a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Da yake jawabi wurin taron karawa juna sani na kwanaki biyu da sashin kula da horaswa na aikace ta rundunar ta shirya a dakin taro na Ogundeku da ke makarantar horas da yaran soji ta kasa da ke Zariya, Babban shugaban rundunar soji ta kasa Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce rundunar sojin na iya bakin kokarin ta wurin sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasa ya daura mata na tafiyar da ayyukan ta bisa doka da oda.

Ya ce, manufar samar da da shirye-shirye irin wannan shi ne domin lalubo hanyoyin magance matsalar tsaro da ta’addanci da ya addabi kasar nan.

Shugaban rundunar wanda Manjo Janar Stevenson Olabanji ya wakilta, ya ce akwai bukatar dakarun sojin Najeriya su kara zage damtse wurin cigaba da sanya kansu a gudanar da harkokin wasanni na yau da kullum.

Ya ce ya jima yana bibiyan irin ayyukan da ake gudanarwa a wannan bangare tun lokacin da ya zama shugaban rundunar soji, kuma zuwa yanzu ya gamsu da cigaba da ake samu ta wannan fuska.

Tunda farko dai babban bakon ya mika ta’aziyyar sa ga al’ummar masarautar Zazzau bisa rasuwar Marigayi Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, Kuma ya yaba wa al’ummar masarautar da mazauna Zariya bisa hadin kai da goyon baya da suka ba dakarun sojin Najeriya da ke aiki a yankin.

Shi ma a jawabin sa, Daraktan sashin kula da horaswa na aikace Manjo Janar Wilson Ali, ya yaba ma irin goyon bayan da suke samu ne daga shugaban rundunar soji duk da kalubalen da ake fuskan na rashin tsaro da kuma annobar Covid-19 da ya addabi sassan kasar nan.

Kuma ya yaba mashi saboda samar da muhinman kudaden tafiyar da ayyukan bangaren.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog