Labarai

Covid-19: Barau Jibrin ya bai wa Kano Naira miliyan 4, Gaya da Shekarau sun bayar da miliyan 4

Sanatan Kano ta Arewa, Barau I Jibrin Maliya, ya baiwa gwamnatin jihar Kano gudunmawar Naira miliyan 4 domin yaki da cutar Coronavirus.

Haka zalika takwarorinsa guda biyu, Mallam Ibrahim Shekarau da Kabiru Ibrahim Gaya sun bayar da Naira miliyan 2 kowannensu.

DABO FM ta tattara cewar Sanatocin jihar sun bayar da kudaden ne zuwa ga asusun da gwamnatin jihar Kano ta bude domin yaki da Coronavirus, kamar yadda mataimakin gwamnan Kano a fannin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana.

Hakazalika, yace sauran ‘yan majalissun wakilai dake jihar sun hada Naira miliyan dai-dai domin sakawa a cikin asusun taimakawar.

DABO FM tattara cewar Dattijo kuma attajiri, Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya bai wa gwamnatin gudunmawar naira miliyan 300 duk dai domin yaki da cutar Coronavirus.

Karin Labarai

Masu Alaka

Zaben2019: Ina kiran magoya bayana da su zabi shugaba Buhari – Salihu Takai

Dabo Online

Ganduje ya bijirewa umarnin Kotu, ya nada sarakuna 4 daya ƙirƙira

Dabo Online

Dokar hana cakudar Maza da Mata a baburan ‘Adaidaita Sahu’ tana nan daram – Ibn Sina

Dabo Online

Yanzu-Yanzu: Mahaifin matashin da baturiya ta biyo Kano zai kai maganar gaban jami’an tsaro na ‘SSS’

Muhammad Isma’il Makama

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da aikin tituna da rijiyoyin burtsate a guraren da za’a sake zabe

Dangalan Muhammad Aliyu

Zan kashewa karamar hukumar Dala naira miliyan 500 -Yakudima

Muhammad Isma’il Makama
UA-131299779-2