Labarai

Muna tare da kai wajen yakar rashin gaskiyar shugabanni – Matar Nelson Mandela ga Sunusi

Uwargidan tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Nelson Mandela, Misis Graca Machel, ta bayyana rashin jin dadinta bisa ga tsige Sarkin Kano murabus da gwamnatin jihar Kano tayi a ranar Litinin.

A cikin wata takardar taya jimami da uwargidan Mandela ta aike Mallam Muhammadu Sunusi II, ta bayyana cewa suna tare dashi a wajen fafutukar yakar yin rashin gaskiya da ya addabi Arewacin Najeriya.

DABO FM ta tattara cewar Uwagidan Mandela tace tana tare da Sarkin Kano murabus a kokari da hazaka da yake da ita wajen fadawa wadanda suke rike da madafun iko gaskiya a ko da yaushe.

A takardar tace, Ina mai matukar rashin jin dadi bisa sauke da akayi daga kan aikinka na Sarkin Kano.”

Na aiko maka da wannan sakon ne domin nuna maka goyon baya wanda nake fatan zai kara maka kwarin gwiwa, ba kai kadai bane a wannan kokarin da kakeyi na yakar rashin gaskiya da takurin da ya dabaibaye yankin Arewacin Najeriya.”

“Ana da tsananin bukatar muryarkar a matsayinka na namiji, shugaban gargajiya da masanin addini wajen fada da yakar abinda yake yi wa mutane ciwo ba iya Najeriya ba har Afirika gaba daya.

“Jajircewarka ta kai ka matsayin da kake saka shugabannin laifukansu tare da yin abinda zai saka su inganta rayuwar mutanensu.”

UA-131299779-2