Labarai

Sanusi ya amince da zama uba kuma shugaban babbar jami’ar jiha ta Kaduna – El-Rufa’i

Gwamnatin jihar Kaduna ta nada Muhammadu Sanusi II (Murabus) a matsayin ‘Chancellor’ na babbar jami’ar jihar Kaduna, Kaduna State University (KASU).

Majiyar DABO FM daga TheCable ta bayyana sanarwar ta fito daga Muyiwa Adekeye, mai Magana da yawun gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i a maraicen Laraba.

Wannan yana zuwa ne bayan wani nadin da jihar Kadunan tayi wa tsohon sarkin Kano a jiya Talata, na mataimakin wata gwaggwabar hukuma a jihar cikin kasa da awa 72.

UA-131299779-2