Labarai Siyasa

Buhari ne yayi umarnin tsige Sarki Sunusi – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Engr Dr Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana shugaba Muhammadu Buhari akan wanda yake da alhakin tube rawanin Sarkin Kano mai murabus, Mallam Muhammadu Sunsusi II.

Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin wata ganawarshi da sashin Hausa na BBC a jiya Talata bayan da yake tofa albarkacin bakinshi tin bayan tube rawanin Sarkin da gwamnatin Kano tayi a ranar Litinin.

DABO FM ta tatattara cewar Kwankwaso bayyana cewar shugawabannin gwamnati ne suke cewa umarni aka basu.

“Shugabannin gwamnatin Kano su da kansu ne ke cewa umarni aka basu (na tsige Sarki Sunusi). Shi (Buhari) ya basu umarni.”

Kwankwaso ya kara da zargin maganganun makusantan Buhari da suke cewa shugaban baya saka baki a riingimun cikin gida, inda ya bayyana cewa shugaba Buhari yana tsoma baki a cikin rigingimun, sai dai yace “Sai dai musamman mu nan a Kano yadda muke gani, (Buhari) yana hargitsa inda yake sa hannu.”

Tsohon gwamna Kwankwaso yace: “Shugaba Buhari yana tsoma hannu cikin akl’amuran jihar Kano. Inda ya kamata ya sa hannu sai mu ga ba nan ya sa hannu ba, inda kuma bai kamata ya sa hannu ba, sai mu ga nan ya yake sa hannu.”

A shekarar 2014, Engr Kwankwaso a wancen lokacin ya nada Sarki Muhammadu SUnusi II bayan rasuwar mai martaba Sarki Ado Bayero wanda ya shafe shekaru 50 yana mulkin kasar ta Kano.

Sai dai alakar gwamnatin Dr Abdullahi Umar Ganduje da Sarki mai murabus, Mallam Muhammadu Sunusi II batayi kyau ba, ta kuma kara tsamari a dai dai lokacin da ake gudanar da zaben gwamna na 2019 inda gwamnatin ta zargi Sarkin mai murabus da goyon bayan dan takarar jami’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Kwankwaso ya bayyan tsige Sarki Sunusi da abin bakin ciki babba inda yace “dama shi mai martaba sarki, mutum ne na duniya gaba daya.”

Ya kuma bayyana cewar duk gwamnatin da ta san yakamata bazata tube rawanin Sarki mai murabus Muhammadu Sunusi II ba tare da nesanta kallon da ake yi wa tsohon Sarkin da mutum mai surutu.

Da yake amsa tambaya game da zargin wasu daga yan Kwankwasiyya da suke kara hura wutar rikicin, shugaban Kwankwasiyyar yace su basa goyon bayan kowa sai bangaren gaskiya.

Ya bayyana cewar iyakar saninsa kamar yadda jami’an gwamnatin suke fada, Sarki Sunusi ya gamu da fushinsu ne saboda yace wanda yaci zabe a bashi nasararsa.

Masu Alaka

Ganin sabon dan majalisar PDP da ya kayar da Kofa tare da shugaban APC ya jawo cece-kuce

Muhammad Isma’il Makama

Kwankwaso ya nuna takaici da bakin ciki akan kashe-kashe da sace-sacen Mutanen Arewa

Dabo Online

Kiru/Bebeji: Baza mu mara wa Kofa baya ba a zaben ranar Asabar -Dattijan APC

Muhammad Isma’il Makama

Aisha Kaita: Shekaran jiya tana PDP, jiya ta shiga APC, yau tayi tsalle ta koma PDP

Muhammad Isma’il Makama

KANO: Ziyarar Atiku, alamar nasara ce?

Dangalan Muhammad Aliyu

Nine Malamin Sanata Kwankwaso a Siyasa – Musa Iliyasu Kwankwaso

Dabo Online
UA-131299779-2