Labarai

Musulman China: Kasar China tana da ikon kulle su – Yariman Saudiya

Biyo bayan tsamari da cigaba da tsare musulman kabilar Uighur dake a lardin Xinjian da kasar China take yi yasa akayi waiwaye zuwa wata magana da yariman kasar Saudiyya, Muhammad dan Salman, yayi tin a watan Fabarairun 2019.

A wancen lokacin, yarima Muhammad dan Salman, ya bayyana cewa abinda kasar ta China take yi yana kan dai-dai.

Jaridar Telegraph ta kasar Birtaniya, a ranar 22 ga watan Fabarairu, ta rawaito yarimnan yana cewa; “Kasar China tana da ikon daukar mataki domin yakar ta’addanci domin kula da tsaronta.”

Yariman ya bayyana haka a gidan Talabijin na kasar China a yayin da yaje kasar domin sanyan hannu a wani sha’anin kasuwancin miliyoyin daloli.

Kasar China ta zargin Musulman da goyan bayan ta’addanci a yankin. Hakan yasa aka zargin kasar ta China da kulle musulmai sama da miliyan 1 a sansanin tare da azabtar dasu, kamar yacce rahotanni suka bayyana.

Sai dai ita kasar ta China ta karyata wannan zargin inda tace maganar ba ta da tsuntsu ba ta da tarko.

DABO FM ta tattaro cewa duk da kasar ta karyata zargin, ta hana duk hukumomi da yan jaridar duniya su shiga sansani da ake ajiyar musulaman, haka kuma sun dana na’urorin da zasu hana ganin abinda yake wakana a cikin sansanin.

A makon da muke ciki ne dai kasashen Musulmai suka gudanar ta taro a kasae Malaysia domin kawo karshen lamarin, sai dai kasar Saudiyya bata halarci taron ba, ta kuma tursasawa kasar Pakistan kauracewa taron.

Kasashe irinsu Turkiyya, Iran da Qatar sun halarci taron.

Karin Labarai

UA-131299779-2