Mutane 30 daga cikin wadanda Ganduje yayiwa aikin ido a unguwar GAMA sun makance

Mutane ne 30 ne daga cikin wadanda suka amfana da shirin aikin idanu kyauta a unguwar Gama dai dai lokacin yin zagaye na biyu a zaben gwamnan jihar Kano.

Dabo FM ta binciko wani rahoto daga gidan rediyon Arewa 93.1, inda mutanen da iftila’in ya rutsa dasu suka bayyanawa gidan rediyon a jiya Juma’a.

Latsa “Play” domin kallon rahotan

Gidan Rediyon ta tattauna da mutane da iftila’in ya shafa inda suka bayyana yacce al’amarin ya faru.

“Wani dattijo mai shekara 60 na haihuwa, mai suna Mallam Yusuf Adamu ya bayyanawa rediyon yadda abin ya kasance dashi.

Mal Yusuf yace “Kwana 3 bayan da akayi mana aiki, naji kamar tsakuwa a ciki, sai yaki (Ido) yaki buduwa, ruwa ya fara zuba, daga wannan ranar har yanzu bansamu kai na ba, bana iya gani, bana iya Bacci.”

“Ni da kaina na kirawo likitan, nace kaga aikinmu ya lalace me kaga za’ayi akai? Su kace aiki ne aka saka su dama kuma sunyi sun gama.”

Majiyoyin DaboFM sun rawaito cewa daga cikin wadanda gidan Rediyon ARewa ya tattauna dasu sun hadar da; Hajiya Amina Mai Icce da Binta Abdu Dan Lamido.

Haj Amina ta shaida cewa; “Ina ciki wadanda akayiwa aikin, da dai kalau ido na yake, ba wani abinda ke damuna, amma tinda akayimin aikin nan shikenan bansamu lafiya. Idona, Kwibi da Hakorina duk ciwo sukeyi. A ido daya akamin aikin, shi kuma yanzu ya mutu. Nace asibitin ance min ya mutu.”

Itama Haj Binta Abdu ya bayyana; “Da dai ina gani da ido na kalau, amma yanzu daga baya yana ciwo, yana min ruwa da zafi. Mijina ya rasu, gani da yara dayawa, muna kira da ataimaka mana.

Sai dai dukkanin kokarin da akayi wajen tuntubar tsagin gwamnati da cibiyar data gudunar da aikin ya ci tura.

%d bloggers like this: