Gwamnan jihar Bauchi ya bada umarnin biyan dukkan ma’aikatan jihar albashin da suke bi

Gwamnan jihar Bauchi, Sen Bala Muhammad ya bada umarnin biyan albashi ga dukkanin ma’aikacin da yake bin gwamnatin jihar.

Wata sanarwa da ofishin gwamnan ya fitar ranar Juma’a tace lallai a biya ma’aikatan jihar dukkanin wani kudi da suke bin gwamnain jihar.

Hakan na zuwa ne kwanaki 2 bayanda aka rantsar dashi a matsayin sabon gwamnan jihar.

“Gwamna ya bada umarnin biyan dukkan ma’aikatan gwamnatin jihar Bauchi daga yau Juma’a 31 ga watan Mayu, 2019 zuwa ranar Litinin, 3 ga watan Yuli, 2019.

Sai dai gwamnan yayi umarni da kada a biya ma’aikatan da aka dauka daga watan Afrilun 2019 zuwa Mayu 2019.

“Babban akanta ya tabbatar ba’a biya ma’aikatan da aka dauka daga watan Afirilu da Mayu ba.”

Bala Muhammad ya bada tabbacin kula da ma’aikatan jihar tare da yin duk mai yuwuwa wajen tabbatar da jin dadinsu a cikin sabuwar gwamnatin jihar ta Bauchi.

%d bloggers like this: