Labarai

Yadda dan majalisar Sokoto ya koma ga Allah bayan ya yanke jike ya fadi a majalisa

A yau Litinin ne aka yi jana’iazar Honarabul Isa Harisu Kebbe dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Kebbe a majalisar dokokin jihar Sokoto bayan ya yanke jiki ya fadi a lokacin da suke shirin fara zaman majalisar na yau.

Abokin aikinsa a majalisar Honorabul Bello Isa Ambarura ya shaida wa BBC cewa marigayin ya yanke jiki ya fadi ne yayin da suke tsaka da hira tare da abokan aikinsa a ofishin mataimakin shugaban majalisar.

“Muna zaune muna hira a ofishin mataimakin shugaban majalisa, shi ne ma ke bayar da labari, wallahi kawai sai ya yanke jiki ya fado daga kan kujera”, Honarabul Bello Isa ya bayyana.

Ya kara da cewa ba shi da wata masaniya kan ko marigayin yana da tarihin wata rashin lafiya, amma tun da suke a majalisa bai taba jin cewa ya kwanta a asibiti ba saboda wata cuta.

“Karfe 10:30 muke shiga majalisa. Muna zaune tare da shi muna jiran sauran ‘yan majalisar da misalin karfe 10:00, sai ake tsokanarsa cewa Isa Harisu ba ya son zuwa da wuri amma yau ya riga kowa zuwa.

“Hirar 2023 muke yi (shekarar babban zabe na gaba a Najeriya) ba wani abin bacin rai ba, ba ma cikin zauren majalisa muke ba.

“Da yake akwai wani dan majalisa masanin kiwon lafiya cikinmu, shi ne ya rika kula da shi kafin a garzaya asibiti, amma da muka buga waya sai aka shaida mana cewa ya rasu.”

Bello Isa ya bayyana marigayin a matsayin mutum “mai faran-faran da mutane” kuma dattijo, wanda “kowa ke haba-haba da shi”.

Marigayi Honarabul Isa Harisu Kebbe dan jam’iyyar APC ne mai adawa a jihar Sokoto. Ya bar mata uku da kuma ‘ya’ya 20.

Masu Alaka

Sokoto: ‘Yan PDP 100,000, sun sauya sheka zuwa APC

Dabo Online

Anyi baikon Yaro dan shekara 17, da Amaryarshi ‘yar 15 a jihar Sokoto

Dangalan Muhammad Aliyu

Zaben Gwamna: Jami’an tsaro sun damke wata mota dankare da kudade a Sokoto

Dabo Online

Rikici ya barke tsakanin Bafarawa da Wamakko a filin jirgin sama na Sokoto

Muhammad Isma’il Makama

Ganduje na cikin jerin gwamnonin dake fuskantar barazanar tsigewa daga kotun ƙare kukan ka

Muhammad Isma’il Makama

Wasu Ɓata-Gari sun guntule hannun Matashi bayan sun Kwace masa Babur a Sokoto

Dabo Online
UA-131299779-2