//
Wednesday, April 1

Duk da bashin $84b, babu laifi dan mun kara ciyo wa ƴan Najeriya $30b – Ministan Yada Labarai

Google+ Pinterest LinkedIn Tumblr +

Duk da cewa akwai bashin dala biliyan 84, Ministan yada labarai, Lai Mohammed ya bayyana babu wani abin cece-kuce kan ciwo bashin da Shugaba Muhammad Buhari yake so yayi na ciwo bashin dala biliyan 30.

Ministan ya bayyana hakan ne ayau Litinin a yayin da ake wani taron fito da manyan abubuwa da Gwamnatin Buhari tayi a cikin shekarar data gaba ta a Abuja. Kamar yadda TheCable ta bayyana.

Dabo FM ta jiyo Ministan na cewa a yanzo ana bin Najeriya bashin dala biliyan 84 ne, inda ya bayyana cewa Gwamnatocin baya ne suka ciyo.

Mutane da dama dai sunyi suka kan sabon bashin da Gwamnatin ke son ciyowa, sai dai Shugaba Muhammad Buhari ya bayyana a cikin wasikar daya aike cewa tilas Gwamnati nada bukatar wadannan kudade don cigaban Najeriya.

Masu Alaƙa  Shugaba Buhari ya kai ziyarar bude aikin gwamna a jihar Ogun

Karin Labarai

Share.

Comments are closed.

%d bloggers like this:
DABO FM 2020