Salihu Sagir Takai ya fice daga jami’iyyar PRP zuwa APC

Karatun minti 1
Salihu Takai da Ganduje
(D)Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje , (H) Salihu Sagir Takai

Dan takarar gwamnan jihar Kano na jami’iyyar PRP a zaben 2019, Mallam Salihu Sagir Takai, ya bar jami’iyyar PRP zuwa APC mai mulkin jihar Kano.

Tin dai a jiya Litinin, hotunan dan takarar da gwamnan jihar Kano, Dr Ganduje suka yi ta yawo a shafukan sada zumunta.

Da yake tabbatar da al’amarin, mai magana da yawun dan takarar, Abdullahi Musa Huguma ya tabbatar cewa Mallam Salihu Sagir Takai, ya sauya sheka daga PRP zuwa APC a ranar Litnin.

Ya kara da cewa basu bar jami’iyyar sai bayan da ya tuntube al’ummar dake goyon bayanshi.

DABO FM ta tattara cewa Salihu Takai ya tsaya takarar gwamnan jihar Kano sau 3.

Ya tsaya a zaben 2011 karkashin jami’iyyar ANPP, inda ya yi rashin nasara a hannun jami’iyyar PDP da dan takararta Rabiu Musa Kwankwaso.

A shekarar 2015, Takai ya sake tsayawa takarar gwamna a jami’iyyar PDP, ya sha kayi a hannun jami’iyyar APC da dan takararta Abdullahi Umar Ganduje.

Kazalika a shekarar 2019, Salihu Takai ya tsaya a jami’iyyar PRP, ya zo a mataki na 3 a bayan Abdullahi Ganduje wanda ya lashe zabe a APC da Abba Kabir Yusuf na PDP wanda yazo na 2.

Kafin tsayawarshi takarar gwamna a ANPP, ya rike mukamai da suka hada da Kwamishinan Ruwa, Raya karkara da Kwamishinan Kananan hukumomi duk a jihar Kano a lokacin mulkin Mallam Ibrahim Shekarau.

Ya kuma yi shugaban karamar hukumar Takai daga shekarar 1999 zuwa 2002 a karkashin inuwar APP.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog