/

NARICT Cibiya ce da al’ummar Arewa ke alfahari da ita-Kwamared Jibrin Salihi

dakikun karantawa

Shugaban Cibiyar binciken sinadarai ta Kasa da ke Zaria wato National research institute for chemical technology (NARICT) Farfesa Joeffry T Barminas, ya jaddada kudirin Cibiyar sa na cigaba da taya gwamantoci a kowanne mataki wurin yaki da cutar sarkewar numfashi ta Covid-19.

Ya bayyana haka ne da yake kaddamar da bada sinadaran tsaftar jiki da na muhalli ga wata Kungiyar matsa mai fafutikar wayar da kan Jama’a game da cutar Korona.

Ya ce, tun da Najeriya ta samu bullar cutar a karo na farko, Cibiyar ta sanya masana da suke aiki karkashin ta, su lalubo hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar. Kuma bisa dogon nazari da kwararrun masu bincike da Cibiyar ke da su, suka samu nasarar samar da sinadaran wanke hannu na shafawa da na fesawa da man shafawa a jiki da kuma na fesawa a iska.

Kuma suka kaddamar da shi a makwannin da suka gabata.

Daga cikin hade-hade da suka yi, sinadaran na magungunan kashe kwayoyin cuta daban-daban ba cutar Korona kadai ba, shiyasa ma suke da zimmar samar da karin magungunan da al’umma za su cigaba da amfanuwa da su.

Sai dai Farfesa Joeffry ya koka da rashin isassun kudade da ke kawo masu cikas wurin gudanar da binciken, Wanda ya ce, suna fatan matukar gwamanti ta shigo ta taimaka masu, za su kara samun karfin gwiwan samar da karin sinadaran tsaftar jiki da na muhalli a ko’ina da ke fadin kasar nan.

Ya yi kira ga mahalarta taron sun yi amfani da abubuwan da suka gani wurin tallata kokarin da Cibiyar ta NARICT ta yi, domin hakan zai jawo hankalin ‘yan kasuwa da sauran hukumomin da abun ya rataya kan su.

Ya jaddada aniyar Cibiyar ta binciken sinadarai ta Kasa da ke Zariya wurin bada cikakken hadin kai da goyon baya ga shirye-shiryen Kungiyar matasa masu rajin wayar da kan al’umma domin yaki da cutar Covid-19.

Da yake nashi jawabin, shugaban Kungiyar Kwamared Jibrin Sulaiman Salihi, Ya ce abun da suka gane ma idon su a NARICK ya kayatar da su matuka, kuma ya kara masu kaimi da azama wurin bada tasu gudunmuwar domin domin yaki da cutar Covid-19.

A cewar shi, sun aiwatar da shirye-shiryen da dama a baya, Amma yanzu ne suke sa ran kara ninkawa a kan kokarin su na wayar da kan al’umma domin yaki da cutar Covid-19.

Kuma ya sake tabbatar da kudirin Kungiyar, na bada hadin kai da goyon baya domin kaiwa ga gaci tare da tallata sinadaran da NARICT ta samar ga kwamitocin yaki da cutar Korona na matakai daban-daban.

Kwamared Jibrin Salihi Ya kara da cewa, NARICT cibiya ce da dukkanin al’ummar Arewa ke alfahari da ita saboda kwarewa wurin binciko nagartattun sinadarai ba wai na yaki da cutar Covid-19 ba kadai.
Kuma ya yi fatan ta nunka kan kokarin da suke da shi yanzu haka, domin al’umma na gani a kasa.

Ya yaba ma shugaban Cibiyar Farfesa Joeffry Barminas saboda yanda yake jagorancin Cibiyar ba tare da nuna wani ban-banci ba, Kuma ya ce a shirye suke su tallafa domin samun nasarar abubuwan da aka sa ma gaba a Cibiyar.

Karin Labarai

Sabbi daga Blog