Labarai

Next Level: Gwamnatin Tarayya ta aminta da fara aikin titin Jirgin Kasa na Ibadan-Kano

Gwamnatin Najeriya ta aminta da yin hanyar jirgin kasa daga garin Ibadan zuwa birnin Kano akan kudi dalar Amurka biliyan 5.3.

Ministan harkokin sufurin Najeriya, Rotimi Ameachi, ne ya sanar da haka a yayin wani taron masu ruwa da tsaki a sha’anin sufurin ruwa wanda da aka gudanar a ranar Alhamis.

“Jiya-jiyan nan muka samu amincewar gwamnati domin karasa titin jirgin kasa na Ibadan zuwa Kano akan dala biliyan 5.3.”

Wata sanarwa data fito daga ma’aikatar sufurin ta bayyana cewa babban Minista Ameachi, zai kula da bangarorin titin jiragen kasa, yayinda karamar Ministar Sufuri, Gbemisola Saraki, zata jagoranci bangaren sufurin ruwa.