(function(w,d,s,l,i){w[l]=w[l]||[];w[l].push({'gtm.start': new Date().getTime(),event:'gtm.js'});var f=d.getElementsByTagName(s)[0], j=d.createElement(s),dl=l!='dataLayer'?'&l='+l:'';j.async=true;j.src= 'https://www.googletagmanager.com/gtm.js?id='+i+dl;f.parentNode.insertBefore(j,f); })(window,document,'script','dataLayer','GTM-P27NM8L');

Niger: Alkali ya yankewa Dan Luwadi hukuncin biyan tarar N30,000 bayan lalata duburar yaron shekara 12

Karatun minti 1

Alkali a wata kotun dake da zama a jihar Niger, ya yankewa wani matashi da yayi luwadi da yaro dan shekarar 12 hukuncin tarar 30,000 da zaman gidan kaso na wata 1 kacal.

Matashin mai suna Abubakar ya turmushe wani yaro mai suna Aminu dan shekara 12 inda ya rinka yi masa lalata  har sai da ya ratattaka masa dubura wanda hakan yai sanadiyar rasa ransa.

Al’amarin ya farune a garin kwantagora na jihar Neja.

Gidan Talabijin na NTA a jihar ta bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar al’amarin.

Matashi ya sace dauke yaron ne yakai shi gidan da yake masa luwadin, lamarin daya janyo hankalin makotanshi suka kirawo jami’an ‘yan sanda.

Gidan NTA ya rawaici cewa dai tuni ‘yan sanda suka kame matashi inda aka garzaya da yaron asibiti domin karbar taimako.

Bayan kaishi asibitin da wasu sa’o’i Aminu yace ga garinku nan.

A bangaren yan sandan kuma, sun gurfanar da matashin a gaban Kotu domin karbar hukunci.

Saidai alkalin ya yankewa Abubakar hukuncin zaman gidan kaso tare da biyan tarar Naira 30,000 kacal.

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog