Nafi gwamnatin Buhari amfani a wajen talakawa da al’ummar Najeriya – Buba Galadima

Buba Galadima, Dan gwagwarmaya, shugaban tsagin R-APC, daga cikin masu ruwa da tsaki a tafiyar Alhaji Atiku Abubakar, yace yafi yiwa talakawan Najeriya amfani akan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari.

Buba Galadima yayi wannnan kalamine a wata tattaunawarshi da sashin Hausa na BBC. Yayi hirar ne sa’o’i kadan bayan rantsar da shugaba Muhammadu Buhari.

Dabo FM ta tattaro Buba Galadima yana cewa ; “Idan baka sani ba, ni nafi yi wa talakawa da al’ummar Najeriya alheri akan gwamnatin Najeriya.”

Buba Galadima ya bayyana cewa babu abinda shugaba Buhari zai iya tabukawa a zangon mulkinshi na biyu bayanda aka rantsar dashi ranar Laraba, 29 ga Mayu, 2019, domin sake jan ragamar kasar a shekaru 4 masu zuwa.

“Ai rana ba ta karya, sai dai uwar ‘ya…. mu gani a kasa mana. Babu abinda zai iya yi.”

“Bazai iya ba. Mutumin da bai iya sauya wa minista mukami ba ko da ya saci Najeriya, ko Buhari da kansa ya sata. Yaushe zai sauya wani ya kawo wani mutum.?

“Na kusa dashi sun riga sun kange shi, ba ya iya jin gaskiya. Yanzu wannan maganar sai ace Buba makiyin kane.”

Buba Galadima yace “Sauke kayanka ka gyara bai nuna sauke mu raba ba.”

%d bloggers like this: