Abdullahi Umar Sani Fagge, Abdulmalik Ja’afar Mahmud – ‘Ya’yan malaman Kano da suka rasu a makon nan

Karatun minti 1

A cikin wannan makon da muke bankwana da shi, an samu rashin wasu daga cikin ‘ya’yan fitattun malaman Musulunci na jihar Kano.

DABO FM ta tattara cewar ‘dan Sheikh Dr Umar Sani Fagge da ‘dan Marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam ne suka rasu.

Abdullahi Sheikh Umar Sani Fagge da akewa lakabi da Yayan Baba, ya rasu ranar Talata 6 ga Oktoba/ 22 ga Safar a unguwarsu ta Fagge bayan fama da matsakaiciyar rashin Lafiya.

(H) Sheikh Umar Sani Fagge – (D)Marigayi Abdullahi Umar Sani Fagge

Kazalika yau Asabar, DABO FM ta samu rahotannin rasuwar Abdulmalik  Ja’afar Mahmud Adam, da a wajen marigayi Sheikh Ja’afaru Mahmud Adam.

 

Karin Labarai

Dangalan Muhammad Aliyu

•Sublime of Fagge's origin.
•PharmD candidate

Sabbi daga Blog