Labarai

Phoebean Ajibola Ogundipe, mawallafiyar littafin ‘Brighter Grammar’ ta rasu da shekaru 92

Mawallafiyar fitaccen littafin turanci na Brighter Grammar, Phoebean Ajibola Ogundipe, ta rasu da shekaru 92.

Mawallafiyar ta rasu ne a birnin Carolina ta Arewa a kasar Amurka ranar 27 ga watan Maris na 2020 kamar yadda makusantanta suka sanar.

Mawallafiyar tayi shura wajen rubuce-rubucen turanci da suka taimakawa dalibai a nahiyar Afrika, daga cikin wasu litattafan da ta rubuta ‘New Practical English for Senior Secondary School’.

Ta rasu ta bar ‘ya’ya 4 da jikoki 10.

Kafin rasuwarta ta kasance mataimakiyar babban mashawarcin gwamnatin Najeriya kan harkar Ilimi. Ta kuma yi babbar sakatariyar Hukumar kyautata ilimi da kimiya da al’adu ta majalisar dinkin duniya a Najeriya. 

Phoebean Ajibola Ogundipe ta kuma karbi lambar girma ta OON a shekarar 1979, ta kuma kafa makarantar kwarewa a kan harkar Ilimi bayan tayi ritaya.

Karin Labarai

Masu Alaka

Mahaifin Hafsat Idris ‘Barauniya’ ya koma ga Allah

Dabo Online

Zamfara: Sarkin Kaura Namodi, Ahmad Muhammad Asha ya rasu

Dabo Online

Alhaji Shehu Shagari ya cika shekara 1 da rasuwa

Dangalan Muhammad Aliyu

Tsohon dan Majalissar jiha na karamar hukumar Sade ta jihar Bauchi ya rasu

Dabo Online

Dan Najeriya ya rasu jim kadan bayan kammala karatun Digiri na 2 a kasar Indiya

Dabo Online

Matashin da yafi kafatanin mutanen duniya gajarta ya mutu a kasar Nepal

Dabo Online
UA-131299779-2