0
Hukumar dake kula da cututtuka ta Najeriya, NCDC ta sake tabbatar da samun karuwar masu dauke da cutar Covid-19 guda 4 da safiyar yau Talata.
Kamar yadda hukumar ta bayyana a shafinta na yanar gizo gizo da shafin Twitter, tace adadin wadanda aka tabbatar a Najeriya ya zama 135.
“A daren yau da misalin karfe 11:00 na safe an sake samun masu dauke da cutar ‘Corona Virus’ guda 4. An samu guda 3 a Osun, 1 a Ogun.”
Ga jerin adadin da aka tabbatar a kowacce jiha;
- Lagos – 81
- Abuja – 25
- Ogun – 4
- Inugu – 2
- Ekiti – 1
- Oyo – 8
- Edo – 2
- Bauchi – 2
- Osun – 5
- Rivers – 1
- Binuwai – 1
- Kaduna – 3
