Paul Pogba ya shiga ‘yar matsala da mai horar da kungiyar dan kasar Portugal (Jose Mourinho). Sai dai bayan barin mai horaswar daga kungiyar Manchester United, dan wasan ya dawo da martabarshi a idon duniya duk da ana ganin tsarin Mourinho ne ya kashe dan wasan.
Pogba ya ci kwallaye hudu a wasa uku daya buga karkashin Solskjaer, wasannin sun hada da wasan satin nan da wanda kungiyar ta kara da kungiyar cardiff, a yau lahadi ma dan wasan ya sake jefa kwallo biyu a wasan da suka kara da kungiyar AFC Bournemath.
Man Utd vs Cardiff – Pogba ya zura kwallaye biyu
Man Utd vs AFC Bounemath – Pogba ya zura kwallaye biyu
Masana fannin wasanni suna gani mai horarwa Solskjaer ya fi Jose Mourinho iya amfani da Paul Pogba
