Ra'ayoyi

Ra’ayoyi: Jahilci ne amfani da kalmar ‘Hassada’ a siyasa

Umar Aliyu Fagge


Siyasa da adawa abu daya ne a tsarin demokradiyya, babu yadda za ayi daya ya samu ba tare da dayan ba dokar da ta samar da tsarin siyasa ita ta samar da salon adawar siyasa.

Ana yin adawar siyasa ne a duk lokacin da mai rike da madafun iko ya nuna gazawar sa a fili domin ya gyara idan har zai iya gyarawar.


Wasu daga cikin wawayen yan siyasa ko masu yi musu tumasanci sukan yi amfani da kalmar hassada a duk lokaci da aka soki lamirin gwanin su, ba tare da tunanin cewa wataran zasu kasan daga cikin masu adawar ba. Kaga kenan suma sun zama masu hassada kamar yadda suke fadawa wasu a baya, wanda hakan yana nuni da makurar jahilcin mutum a fili tunda har zai iya kiran kansa da dan hassada.


A duk lokacin da wani ya soki lamirin gwaninka a siyasance kokari zaka yi gurin wofantar da wannan suka ta hanyar kawo kayattatun hujjoji wanda mai karatu zai aminta da kai, ba ka huge da cewa ana maka hassada ba wanda hakan yana nuni da cewa kana daya daga cikin wawayen da yan siyasa suke daukar nauyi gurin cin mutuncin mutane kuma duk wanda yaga rubutun ka yasan inda ka dosa.

Babu dan siyasar da yake kaunar ka kamar yadda yake son cigaban yayan sa, babu dan siyasar da zai so rayuwarka ta inganta kamar ta yayan sa to don me zaka ringa aiwatar da shirme da shirirta da sunan kare wan dan siyasa?


Idan don ya baka aiki kake yin haka to ilimink bai bashi da amfani domin wanda ya kame kanshi ko baiyi ilimi ba yafi ka daraja da kima a idon alummar da suka san me suke, babu wani dan siyasa da ya isa yayi maka abin da Allah bai nufe ka dashi ba, g misali nan a fili mutane nawa ne suke bin yan siyasar kamar su bauta musu amma basu yi musu maganin kishiruwa ba?


Ya zama wajibi mutane musamman matasa su kunce igiyar zato tare da nema a taskar ubangiji, wacce bata bukatar sai ka aibata wane sannan ka samu abin da kake nema. Wanda shima baya samuwa sai tillin zunubi da kareraye da ka tarawa kanka ranar hisabi, ka kare karya ka tallata karya don neman abinci.


Rattabawa Umar Aliyu Musa [email protected]07089706026

Karin Labarai

Masu Alaka

Ko faduwar Atiku zata zama tashin Kwankwaso a fafutukar darewa kujerar Lamba 1?

Dabo Online

#JusticeForKano9: Shirun ‘Yan Arewa da Malaman ‘Social Media’ akan mayarda Yaran Kano 9 Arna

Dabo Online

‘Yan siyasa na amfani da kalmar “Hassada” ko “Bakin ciki” don dakushe masu musu hamayya

Dabo Online

Ba Kwankwaso ne basa so ba, cigaban Talaka ne yake musu ciwo – Dangalan Muhammad Aliyu

Dabo Online

Su Waye ke bautar da Matasa a manhajar Facebook?

Idris Abdulaziz Sani

Ko faduwar Atiku zata zama tashin Kwankwaso?

Dangalan Muhammad Aliyu
UA-131299779-2