Labarai

Tirkashi: Gwamnatin tarayya zata hana manyan motoci hawa kan titunan kasar nan

Gwamnatin Najeriya ta dauki aniyar hana manyan motoci hawa kan titunan kasar da zarar ta kammala aiyukan layin dogo.

Majiyar Dabo FM ta rawaito ministan sufuri, Rotimi Amechi ne ya bayyana haka a garin Ikko cikin wani taron tattaunawa kan samar da kayayyakin more rayuwa tare da daukar nauyin su wanda kamfanin Deloitte ya shirya domin nazartar tattalin arzikin kasar mai taken ‘Nigerian Economy Outlook 2020’.

Amechi ya ce “Da zarar mun kammala aikin layin dogo akwai ire iren kayayyakin da baza mu kara bari a dauke su a kan titinan kasar nan ba, ya zama tilas koda kuwa ana so ko ba’aso.”

Ya kuma kara da cewa yin hakan zai sanya titinan Najeriya su yi karko tare da dadewa ana mora. Haka kuma daukar kayan a jiragen kasa zai fi sauri.

Ministan ya kuma shaida wa majiyar mu cewa Najeriya ta aike da mutane 150 domin karatun kere kere musamman a fannin kera hanyoyin jiragen kasa, kana gwamnatin tarayya zata bude jami’o’in sufuri nan gaba kadan.

Karin Labarai

UA-131299779-2