Yadda Ganduje ya taka rawa a taron kaddamar sabon garejin gyaran motoci na mata da maza

A ranar 30 ga watan Janairun 2020, gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya kaddamar da sabon garejin gyara da wanki mota na zamani a karamar hukumar Dawakin Tofa.

Hakan na zuwa ne bayan da gwamnatin jihar ta tura yan jihar 422 domin koyo gyara motoci a kamfanin mota na Peugeot dake jihar Kaduna.

A faifan bidiyon taron, an hangi gwamnan jihar yana taka rawa cikin nishadi a daidai lokacin da yake gwada yadda ake wanke motoci a zamance.

Haka zalika tsohon gwamnan jihar, Engr Rabiu Musa Kwankwaso, ya tura rukunin karshe na daliban da gidauniyar Kwankwasiyya take daukar nauyin karatunsu a kasashen duniya.

Rukunin karshen zasu yi karatun Larabci da fannin addinin Musulunci a kasashen Sudan da Hadaddiyar Daular Larabawa.

Masu Alaƙa  Ni ba Dalar da zaka saka a Aljihu ba kunya bane - Martanin Wike ga Ganduje akan rushe Masallaci

DABO FM ta tattara cewar tin dai a watan Satumba da Oktobar 2019, rukuni na farko da na biyu daga cikin daliban suka sauka a kasar Indiya domin fara karatu.

Karin Labarai

Comments are closed, but trackbacks and pingbacks are open.