Kiwon Lafiya

Rashin gwaji kafin Aure na haifar da matsaloli -Dr Sani Hassan

A kokarin da take na samar wa matasa aikin yi da koyar da su sana’o’i da muhinmancin sanin matakin jini ga bil-adama da kuma wayar da kai game da muhinmancin zuwa domin amfana da wasu darussa na musamman da akan ware lokaci zuwa lokaci ‘extra moral classes’, kungiyar cigaban Al’ummar Kakaki, ta gudanar da taron wayar da kai da zummar fadakar da mazauna yankunan anguwannin Albarkawa da Kakaki da Kofar Fada da kuma Bambale, game da wadannan abubuwa da suka shafi rayuwar Al’umma a yau.

Da yake zantawa da manema labarai a gefen taron, daya daga cikin wadanda suka shirya taron Alhaji Sani Hassan, ya ce, shirya taron na zuwa ne a dai-dai lokacin da duniya ta shiga halin dimuwa akan rashin sanin matsayin jinin dake jiki, wanda kuma hakan ke haifar da matsaloli sosai ga wasu daga cikin ma’aurata.

A cewar sa, saboda kokarin magance matsalar, yasa suka samar da wannan shirin da ake sa ran matasa sama da Dari Uku su amfana. Ya nuna gamsuwar sa matuka kan yadda matasan suka yi na’am da wannan shiri.

A jawabin sa, shugaban taron kuma daya daga cikin iyayen Anguwar Alhaji Ibrahim Abdullahi, ya naimi wanda za su amfana da shi wannan shirin, su yi amfani da shi bisa tsari kuma kamar yadda ya dace, ta yadda a gaba su ma zasu amfanar da masu tasowa.

A jawaban su daban-daban, wasu daga cikin mahalarta taron, Lukman Amin da Hajara Yakubu da kuma Hauwa’u Muhammad, sun bayyana gamsuwar su ne da taron da aka shirya domin su, kuma suka sha alwashin aiki da abun da suka koya domin cigaban su.
Daga nan sai suka gode wa uwar kungiyar ta Al’ummar Kakaki, bisa daukan nauyin wannan shiri tare da tabbatar masu da basu goyon baya akan dukkanin shirye-shiryen su.

Tun farko da suke gabatar da kasidu daban-daban, Dr Ango Abdurahman na FCE Zariya da Alhaji Shehu Na Allah, sun naimi iyaye ne su rika zamewa abokan shawara tare da sanya ‘ya’yan su akan tsari mai kyau musamman a bangaren koyo da koyarwa.

UA-131299779-2